Yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya
June 8, 2012Rahoton da Amurka ta fitar da ke nuna rashin tasirin da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa ke da shi a Najeriya na nuna damuwa a kan irin taɓarɓarewar da cin hancin ke yi a ƙasar duk kuwa da dokoki da ma hukumomin da ke iƙirarin yaƙar masu cin hanci a Najeriya, to shin a ina matsalar take ne kuma ma wace illa wannan ke da shi ga ƙasar.
Koma bayan da ake ci gaba da fuskanta a fannin yaƙi da cin hanci da rashawa musamman gazawar mahukuntan Najeriyar wajen hukunta wanda aka same su da hannu dumu-dumu wajen rub da ciki a kan dukiyar gwamnati saboda zargin kasancewar na kusa da masu riƙe da madafan iko ne ya sake haifar da wannan zargi da Amurikan ta yi, inda ta bayyana hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a matsayin ta jeka na yi ka.
Gazawar da ta bayyana a fili da suka haɗa da yadda aka kame tsoffin gwamnonin jihohin Gombe, Ogun, Oyo da Nasarawa har ma da kaisu kotu amma maganar ke shiriricewa, ga sukurkucewar sashin shari'a inda alƙalai ke karɓar cin hanci da ma gazawar gwamnatin na hukunta waɗanda ake zargi da cin hanci da rashawa na fiye da dalla biliyan 16 a fannin wuta lantarki da ma na baya baya nan na tallafin man fetir. To shin me ke kawo gazawar da ake fuskant ane duk da hukumomin yaƙi da cin hancin da ake da su? Mallam Abubakar Umar ƙari masanin kimiyar siyasar tattalin arziki da ke ke jami'ar Abuja.
To sai dai gazawar da ake kallon hukumar EFFC wajen hukunta waɗanda ake zargi da cin hanci da rashawa matsala ce da Malam Abubacar Othman shugaban ma'aiakata na hukumar ta EFCC ya bayyana da jinkirin da suke fuskanta a kotuna ba wai basa fattataka masu cin hanci a ƙasar bane.
Sanin irin damuwar da ake nunawa a kan wannan matsala da ke zama mummunar ɗabi'a da ke zaizaye ɗabi'un 'yan Najeriya da mayar da mafi yawansu masu halin ɓeraye ya sanya Awwal Musa Rafsanjani na gamayyar ƙungiyar yaƙi da cin hanci da rashawa ta "Zero Corruption" bayyana cewa mafita guda ce ga matsalar.
Ci gaba da ƙememe da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ke yi na kin bayyana kadarar da ya mallaka kamar yadda wanda ya karɓa a hannunsu tsohon shugaban Najeriya marigayi Umaru Musa yar'Adua ya yi da ya zama abin misali, na ƙara jefa tabbaba ga zummar gwamnatin Najeriya na yaƙi da cin hancin da ta daɗe tana iƙirari. Wannan na ƙara bayyana saboda yadda hatta kuɗin 'yan fansho basu tsira ba da aka gano an tafka sata ta fiye da Naira biliyan 200, baya ga na tallafin man fetir, matsalar da ke dabaibayi ga ci gaban Najeriyar.
Mawallafi:Uwais Abubakar Idriss
Edita:Yahouza Sadissou Madobi