1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi da ta´addanci a Yuganda da Kenya

July 17, 2010

A koƙaƙin daƙile ta´addanci a yankin gabacin Afirka, hukumomi a Kenya da Yuganda sun cafke wasu ´yan Somaliya

https://p.dw.com/p/OO6V
farautar ´yan Somaliya a Kenya da YugandaHoto: Simone Schlindwein

Bayan tagwayen hare-haren ta´addancin da su ka wakana a birnin Kampala na ƙasar Yuganda, jami´an tsaron ƙasashen yankin gabacin Afirka, sun shiga cafke-cafken ´yan Somaliya da ke gudun hijira.

Idan dai ba manta ba, ranar Lahadi da a wuce, a yayin da ma´abuta ƙwallon ƙafa a birnin Kampala, ke kallon gasar ƙarshe tsakanin Spain da Holland,sai  kwatsam!!! babu zato babu tammaha, wasu tagwayen bama-bamai su ka tashi, wanda kuma su ka yi sanadiyar mutuwar mutane 73.

Washe gari, Ƙungiyar Al-Shabab mai tsatsauran ra´ayin addinin Islama  a ƙasar Somaliya, ta ɗauki alhakin kai wannan hari.A nasu ɓangare hukumomin Yuganda da na ƙasashe maƙwabta, kamar irin su Kenya su ka bayyana ƙara matsa ƙaimi domin tabbatar da tsaro.

Ministan harakokin wajen Yuganda, Henry Oryem Okelo ya tabbatar da cewa sun cafke wani ´yan ƙasar Somaliya wanda ake kyauttata zaton ya na da hannu a cikin harin, ya ce:Jami´an tsaro sun cafke wasu mutane huɗu.Suma jami´an tsaron  ƙasar Kenya sun ɗamke wasu.A halin yanzu dai komai na tafiya dai dai, kuma dakarunmu na cikin shirin ko ta kwan.

A ɓangaren ƙasar  Kenya ma dai, al´amarin ya fi ƙamari, domin tsakanin  Juma´a zuwa yanzu,´yan sanda sun kama fiye da mutane 100 dukkan su ´yan asulin Somaliya a cikin wata unguwa wadda ´yan gudun hijirar Somaliya su ka yi wa kaka gida.

Evans Morani wani mai sharhi ne game da harakokin siyasa a ƙasar Kenya, ya yi huruci game da wannan saban yanayi da yankin gabacin Afirka ya shiga:

Kenya na cikin halin barazanar fuskantar hare-here daga ƙungiyar Al-Shabab.Bayan abun da ya faru a Uganda,al´umar Kenya ta shiga zaman  zullumi.Ƙasashen duniya sun yi buruss da rikicin Somaliya sun zuba ido su na kallon Al-Shabab na cin karenta babu babbaka.

Ƙasar Kenya saɓanin Yuganda da Burundi, ba ta aika sojoji ba a Somaliya, to sai dai ta na da dakaru cikin ƙungiyar tattalin arzikin yankin gabacin Afirka wato IGAD, wadda a bayan- bayan nan ,ta yanke shawara aika ɗaukin sojojin ga gwamnatin Somaliya, domin taimaka mata ta murƙushe Ƙungiyar Al-shabab.

Su kuwa al´umomin Somaliya da suka samu mafaka a ƙasashe daban-daban na yankin, tun bayan tagwayen hare-haren Yuganda sun shiga halin zaman jini kan akaifa,mussamman ta la´akari da yadda ake nuna su da yatsa, tare da danganta su da ´yan ta´adda.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi