Yaƙin Siriya na ɗaukar sabon salo
January 13, 2014Mayaƙan na ISIL na kuma bin gida-gida suna cafke 'yan tawayen na Siriya da suka yi yunkurin fatattakarsu daga Siriyan da kuma fararen hula da ke goyoyn bayan 'yan tawayen.Masu rajin kare hakkin ɗan Adam da ke sanya idanu a yaƙin na Siriya sun bayyana cewa masu tsatsauran ra'ayin sun yi amfani da Masallatai wajen yin kira ga al'ummar yankin su miƙa makamansu suna masu cewa za su kafa shari'ar Musulunci ne, inda a hannu guda kuma suka kafa shingayen binciken ababen hawa a kan titunan garin na Al-Bab.
Wannan sabon rikicin cikin gida tsakanin 'yan tawayen na Siriya da ke ƙoƙarin ganin sun kifar da gwamnatin Bashar al-Assad, na zuwa ne ƙasa da kwanaki 10 da fara wata tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicn ƙasar a birnin Geniva na ƙasar Switzerland.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane