Yaɗuwar rikicin Siriya zuwa Lebanon
May 26, 2013Wasu makamai masu linzami guda biyu da aka harba a wannan Lahadin (26.05.13), a wata unguwar da galibin mazaunanta nabiya darikar Shi'a ne da ke birnin Beirut na kasar Lebanon, ya janyo rauni ga mutane da dama, kamar yadda mazauna unguwar suka bayyana. Wannan harin dai ya zo ne yini daya kachal bayan da jagorar kungiyar Hizbullah ta mabiya darikar Shi'ah a kasar ta Lebanon, Hassan Nasrullah ya bayyana cewar, mayakansa za su ci gaba da yaki a kasar Siriya har sai gwamnatin kasar a karkashin jagorancin shugaba Bashar al-Assad ta sami nasara.
Harin kuma shi ne irinsa na farko da aka kaiwa yankin da galibinsa mabiya darikar Shi'ah ne a birnin na Beirut, tun bayan barkewar yakin basasa a kasar Siriya, wadda ke makwabtaka da Lebanon, wanda kuma ya kara zafafa yakin bangaranci a cikin gidan Lebanon din.
Duk da cewar babu wani mutum ko wata kungiyar da ta dauki alhakin kaddamar da harin, Brigadier Selim Idris, na kawancen 'yan adawar Siriya da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya ya shaidawa tashar telebijin ta al-Arabiyya cewar babu hannun dakarunsa wajen kai harin, kana ya bukaci 'yan tawayen da su ci gaba da yaki a cikin Siriya kawai ba tare da tsallakawa domin kai hari a wata kasar ketare ba.
A halin da ake ciki kuma ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, ya yi Allah wadai da rikicin da ya barke a Lebanon yana mai cewar bai kamata a kyale rikicin Siriya ya bazu zuwa kasar ba.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman