Yini na biyu a zaɓen ƙasar Indiya
April 17, 2009Kimanin mutane 19 ne da suka haɗa da jami'an tsaro 10 da ma'aikatan zaɓe biyar ne suka rasu, bayan harin da aka kai a wasu a jibiyoyin zaɓe a jihohin a ƙalla bakwai na ƙasar Indiya da wata ƙungiyar 'yan a ware da ake kira Maoists take da karfi.
A yau ne aka shiga kwana na biyu na zaɓen ƙasa a Indiya,ƙasar data fi kowace ƙasa a Duniya yawan masu zaɓe irin na Demkokiraɗiyya. Sai dai kamar kowace ƙasa musanman masu tasowa, itama Indiyan bata tsira daga rigingimun dake tattare da zaɓuka makamantan wa'yannan ba.
Masu zaɓe miliyan 700 ne dai ake sa ran zasu kaɗa kuri'ar su a wannan zaɓe da za'a gudanar cikin makwani huɗu masu zuwa. Sai dai tun kafin tafiya tayi nisa, masu adawa da gwamnatin ƙasar dake neman ɓallewa daga Indiya da ake kira Maoist , sune suka kai hare-hare a jihohin ƙasar da dama, domin kawo cikas ga zaɓukan da ake gudanarwa.
To sai dai duk da wa'yannan hare-haren masu kaɗa kuri'a da yawansu yakai kashi 58 zuwa 62 cikin Ɗari ne suka fito domin zaɓen 'yan takaran jam'iyyu daban-daban na 'yan majalisun da ake dasu a Indiya. Wani jami'in 'yan sandan Indiyan ya bayyana yadda 'yan ƙungiyar ta Maoists suka kai hari ga tawagar wasu jami'an zaɓen a jiya.
yace "Wannan hari ya auku ne a lokacin da jami'an tsaron tare da ma'aikatan da ke ƙoƙarin kaiwa ga tashoshin zaɓen ne. Wato bayan da suka shiga wata motar Bas, kuma wannan motar ta Bas ɗinne ce ta taka nakiyar da aka dasa masu akan hanya"
To sai dai a yayin da ake yabawa da fitowan masu zaɓen masu lura da harkokin siyasar ƙasar ta indiya na ganin hare-haren 'yan ƙungiyar a raban a yankunan da ta fi karfi ya firgita masu zaɓe. Kamar yadda wata mai sharhi akan lamuran siyasar indiyan tayi bayani.
Tace"a gani na ƙungiyar 'yan awaren ta Indiya ta samu nasara firgita masu zaɓe a wannan yanki da suka fi karfi. Ni ina ganin sun sami nasara, duk da cewar ba'a samu nasaran kashe mutane da dama ba, amma sun samu nasarar tsoratasu ta yadda kowa ke tsoron lafiyar sa".
Bayan matakan da hukumomi suka ɗauka na kare jama'a da ma'aikatan zaɓe, su kansu 'yan siyasan basu tsira ba daga fushin jama'a wa'yanda ke jifan 'yantakara da takalma.Al'amarin dayasa da yawa daga cikin 'yantakaran ke gabatar da jawaban su a cikin keji domin kaucewa jifan takalma.
Yanzu dai a yayin da al'umar Indiya dama sauran ƙasashe na Duniya suka zura ido domin ganin yadda sakamakon zaɓen zai kasance tsakanin Jami'yar dake mulki ta kongress data Hindu Bharatiya Janata mai adawa, masu lura da harkokin Siyasar ta Indiya suna ganin da ƙyar ne jam'iyun biyu su samu rinjaye kai tsaye ba tare da ƙawance ba.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Zainab Mohammed