Shirin neman tsige Trump na kara karfi
November 1, 2019A Amirka yunkurin tsige Shugaba Donald Trump daga kan mukaminsa na kara samun tagomashi bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da sauraron bayanan shaidu da ke bukatar bayar da bahasi kan abin da suka sani dangane da zargin da ake yi wa Shugaba Trump na yin amfani da matsayinsa wajen neman Ukraine ta gudanar da bincike kan abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasa na tafe Joe Biden da dansa.
Har kawo yanzu dai 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar Democrates sun saurari wasu jami'an diplomasiyya da kuma mashawartan Shugaba Trump kan zargin da ake yi masa amma ba a bainar jama'a ba. Tuni dai Shugaba Donald Trump da akasarin 'yan majalisa na jam'iyyar Republican suka goya masa baya wajen kada kuri'ar, ya soki lamirin matakin a matsayin bita da kullin siyasa.
Rabon da majalisar dokokin Amirka ta kada kuri'ar amincewa da sauraran shaidu a bainar jama'a kan zargi wani shugaban kasa, tun lokacin bincike neman tsige Shugaba Bill Clinton sama da shekaru 20 da suka gabata.