Yoshiro Mor ya yi katobara
February 11, 2021Talla
Kafofin yadda labarai na Japan da suka ambato na kusa da Mori, sun ce zai yi marabus a ranar juma'a a lokacin wani zaman taron kwamiti. Yoshiro Mori dan shekaru 83 tsohon firaminista daga shekara ta 2000 zuwa 2001 wanda ya saba yin katobara, a makon jiya a cikin wata tattaunawar ya ce mata ba su da dabbarar ko fahimtar yin kammalalen jawabi a lokutan taruka abin da ya janyo tsokaci a ciki da wajen kasar ta Japan.Tun farko a bara aka shirya yin gasar ta wasannin na lokacin bazara, amma aka dage har ya zuwa wannan shekara saboda annobar corona.