Yuganda: An amince da gyaran kundin mulki
December 21, 2017Majalisar dokokin mai mambobi 434 galibi 'yan jam'iyyar NRM ta shugaba Yoweri Museveni da suka mamaye majalisar ne suka amince da gyara ga kundin tsarin mulki domin bayar da dama ga wadanda suka haura shekaru 75 na tsayawa takara a zaben shugaban kasa sakamakon kawar da ayar doka da ke kundin tsarin mulki mai lamba 102B. Amman kuma ba daukacin 'yan majalisar na jam'iyya mai mulki ne ke goyon bayan matakin ba.
Wannan mataki na 'yan majalisar ya share hanya ga Museveni dan shekaru 73 na iya sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2021, ganin sabuwar dokar ta sake dawo da wa'adi biyu na mulki ga shugaban kasa. Har wa yau karkashin sabon matakin shugaba mai ci da ya ke rike da madafun iko tun shekarar 1986 fiye da shekaru Talatin zai iya ci gaba da rike madafun iko zuwa shekara ta 2031. Wannan dai ya sa wasu 'yan majalisa daga yankin arewacin kasar yin barazanar ballewa.
Ana su bangaren al'ummar kasar suna da ra'ayoyi mabanbanta game da matakin, wasu na ganin wannan ba zabin su ba ne face ra'ayin 'yan majalisar kasar wasu kuwa sun yaba da mulkin Museveni sai dai suna fatan demokradiya za ta samu gindin zama a kasar. A wasu kasashen Afirka za a iya cewa demokradiyya ta samun gindin zama amma a wasu kasashe ana fama da shugabannin 'yan tazarce.