An kama Bobi Wine daga wuren taron da gwamnati ta haramta
April 22, 2019Talla
Amfani da karfin da jami'an tsaron kasar Yuganda suka yi wajen tarwatsa magoya bayan Bobi Wine ya haifar da rudani. Wine wanda yanzu dan majalisa ne ya shirya amfani da taron ne don sanar da manema labarai halin da ake ciki bayan da ya karbi umarnin gwamnati kan soke taron bikin.
Sa-in-sa a tsakaninsa da bangaren gwamnati ya soma ne bayan da aka zarge shi da hannu a jifan tawagar Shugaba Yoweri Museveni lokacin yakin neman zaben cike gurbi na majalisar dokoki.
Mawakin da ya rikide ya koma dan siyasa, ya ce shi dai yana gwagwarmaya da Shugaba Museveni ne domin tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki a kasar ta Yuganda.