Yuganda da Ruwanda sun musanta batun 'yan gudun hijira
April 3, 2018Talla
Tun da farko Firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana kin amincewarsa da shirin Majalisar Dinkin Duniya na kara tsugunar da 'yan gudun hijirar da suka fito daga Afirka a kasashen yammacin duniya a wannan Talatar, yayin da yake ganawa da wa su fusatattun jama'a mazauna kudancin birnin Tel Aviv.
A halin yanzu dai Netanyahu na fuskantar Allah wadai daga kungiyoyi daban-daban ciki kuwa har da jam'iyyarsa ta Likud mai mulki a kasar.