1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda ta haramta nuna zanga-zangar 'yan adawa

Suleiman BabayoMay 6, 2016

Yuganda ta haramta nuna zanga-zangar 'yan adawa kai tsaye ta kafofin yada labarai yayin da ake shirin sake rantsar da Shugaba Yoweri Museveni kan sabon wa'adi.

https://p.dw.com/p/1Iix3
Ugandas Oppositionsführer Kizza Besigye
Hoto: DW/E. Lubega

Gwamnatin kasar Yuganda ta haramta yada zanga-zangar 'yan adawa kai tsaye ta kafofin yada labarai, da 'yan adawa suka tsara a mako mai zuwa domin nuna rashin amincewa da zaben da Shugaba Yoweri Museveni da ya kwashe shekaru 30 kan madafun iko ya sake lashewa.

Ministan yada labarai na kasar Jim Muhwezi ya sanar da wannan haramci, kuma ya yi gargadin duk wanda ya saba dokar ka iya rasa lasisin aiki saboda kotu tuni ta bada umurni hana zanga-zangar da 'yan adawa suka nuna tirjiya.

Ranar Alhamis mai zuwa aka tsara sake rantsar da Shugaba Yoweri Museveni na kasar ta Yuganda kan sabon wa'adi, a wani bikin da za a gudanar a birnin Kampala fadar gwamnatin kasar.