Yuganda ta yi barazanar janye dakarunta daga Somaliya
November 3, 2012Yuganda ta yi barazanar janye dakarunta daga Somaliya, a matsayin martani ga zargin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi mata, na rura wutar rikici a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo.
Wani rahoton da komitin Sulhu ya fitar ya baiyana ƙarara cewa, ƙasashen Yuganda da Ruwanda na ɗaurewa 'yan tawayen M23 na Kongo gindi.Rahoton ya danganta Yuganda da matsayin ɓarawan da yayi sata, ake kuma bin sau tare da shi.
Hukumomin Kampala da ke shiga tsakanin a rikicin da ya haɗa gwamnatin Kinshasa da 'yan tawayen M23 sun yi watsi da wannan zargi, wanda suka ce ba shi da tushe.
Ministan tsaron ƙasar Yuganda, Muruli Musaka yayi ƙarin haske:
"Muna daga cikin ƙasashen da suka amince su shiga tsakani a warware wannan rikici, duk da ƙoƙarin da muka yi , sai gashi an saka mana da sharri.Ba za mu amincewa ba da wannan cin zarafi.A yanzu za mu daina duk wani taimakon samun zaman lafiya a cikin wasu ƙasashe."
Za mu maida hankali domin kare ƙasarmu.
Ƙasar Yudanga na da sojoji 6.500 a ƙasar Somaliya, wanda suka taka rawar gani a yaƙi da ƙungiyar Al-Shebab, haka zalika, ta bada runduna mai ƙwari, domin fatattakar 'yan tawaye LRA na Josef Konny.
Ita ma ƙasar Ruwanda ta yi watsi da wannan rahoto, wanda ta ce bai yi mata adalci ba.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal