1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda za ta mika dan tawayen kasar ga kotun duniya

January 13, 2015

Kasar ta tabbatar da cewa za a tisa keyar dan twayen da aka kama zuwan kotun duniya

https://p.dw.com/p/1EJVp
Sudan Kongo LRA Rebellen
Hoto: Stringer/AFP/Getty Images

Rundunar sojin kasar Yuganda ta bayyana cewa daya daga cikin shugabannin 'yan tawayen kungiyar LRA da aka kama zai fuskanci hukunci a kotun duniya mai hukunta masu manyan laifukan yaki da ke birnin Hague na kasar Netherlands.

Kakakin sojin kasar Paddy Ankunda ya tabbatar da cewa za a mika dan tawayen Dominic Ongwen wanda ya mika kai ga sojojin kasar Amirka, kai tsaye daga kasar da aka kama shi a makon jiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, za a tisa keyarsa zuwa kotun ta duniya.

Ongwen zai fuskanci tuhumar laifukan yaki da cin zarafin dan Adam, kan yakin sunkurin kungiyar LRA, yayin da ake ci gaba da neman shugaban 'yan tawayen kasar ta Yuganda, Joseph Kony da taimakon sojojin Amirka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal