1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin karshe na warware rikicin siyasar Gambiya

Gazali Abdou Tasawa
January 19, 2017

Yayin da wa'adin mulkin Shugaba Jammeh ya kare, an shiga halin rashin tabbas kan abin da ka iya faruwa a kasar.

https://p.dw.com/p/2W1oK
Gambia Yahya Jammeh in Banjul
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

A kasar Gambiya 'yan sa'o'i bayan da wa'adin mulkin Shugaba Jammeh ya kawo karshe, yanzu haka Shugaban Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz ya isa a kasar ta Gambiya inda ya gana da Shugaba Jammeh da nufin shawo kanshi na ya mika mulki cikin laluma. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin kasashen Afirka ta Yamma da dama suka isa a kasar Senegal da nufin yin amfani da karfin bindiga wajen tumbuke Shugaba Jammeh idan har hanyoyin diplomasiyyar suka ci tura. 

Babu dai wani bayani kan abin da shugabannin biyu na Gambiya da na Moritaniyar suka cimma a lokacin ganawar tasu. Sai dai tashar talabijin ta gwamnatin kasar ta Gambiya ta ruwaito cewa bayan ganawa da Shugaba Jammeh shugaban Mauritaniyar ya ce ya samu kwarin gwiwa na yiwuwar shawo kan rikicin ta hanyar diplomasiyya. 

A ranar Laraba ne jirgin Shugaban kasar ta Mauritaniya wanda ake bayyanawa a matsayin amini ga Shugaba Jammeh, ya sauka a filin jirgin saman birnin Dakar inda shugaba Macky Sall na Senegal da mai jiran gado na kasar ta Gambiya Adama Barrow suka tarbo shi. Kawo yanzu dai babu wani bayani a game da sakamakon da ganawar shugabannin uku ta bayar.