Yunkurin kubutar da mutane a Nairobi
September 23, 2013Karar makamai da fashe-fashe sun turnike manyan shagunan birnin Nairori na kasar Kenya, inda dakarun kasar ke neman kawo karshen garkuwa da wasu 'yan bindiga suka yi da mutane. Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 68, sannan wasu kimanin 175 sun samu raunuka, bayan kwashe kwanaki uku da garkuwar.
Tuni kungiyar al-Shabaab ta kasar Somaliya ta dauki alhakin kai hari. kuma ana kyautata zaton akwai kimanin 'yan bindiga 10 zuwa 15. An kubutar da mafi yawan wadanda ake garkuwa da su, kuma kusan gini baki daya na karkashin dakarun gwamnati.
Shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta ya yi jawabi wa al'ummar kasar inda ya dauki kudirin hukunta duk wanda yake da hannu cikin lamarin. Ya zuwa yanzu an tabbatar cikin wadanda suka hallaka akwai 'yan kasashen ketare.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe