1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin sauya tsarin shari'ar zabe a Najeriya

April 4, 2014

Majalisar dattawan Najeriya na nazarin wata dokar da ta tanadi Hukumar Zaben kasar mai zaman kanta ta INEC ta tabbatarwa kotunan shari'ar ko zabe ya yi dai dai ko bai yi ba

https://p.dw.com/p/1Bc4z
Wahlen Nigeria Attahiru Jega
Hoto: AP

A wani abun dake zaman kokari na sauya tsarin shari'ar zabuka a tarrayar Najeriya, majalisar dattawan kasar na nazarin wata doka da a karkashinta, Hukumar Zaben kasar mai zaman kanta ta INEC ce za ta dauki alhakin tabbatarwa kotunan shari'ar zabukan kasar fadin komai dai dai.

A baya dai, ga duk mai tunanin tayi baki ga batun zabukan kasar ta Najeriya, babban karatunsa na zaman na kama hanyar kotu da nufin kawo shaidu dama tafka muhawara ta neman hakki, a cikin tsarin shari'ar da ya dorawa mai zargi tabbatar da hujjar zargin nasa.

To sai dai kuma, ta kama hanyar sauyawa tare da wata sabuwar dokar da yanzu haka ke gaban majalisar dattawan kasar, dokar kuma da a karkashinta alhakin tabbatar da shaidar magudi na zabuka ke neman sauyawa daga masu korafi na siyasa ya zuwa ga hukumar zaben kasar da ta sha zargin hada baki da yan siyasa wajen tabbatar da son zuciya a aikin zabe.

Tanadin sabuwar dokar

Abun kuma da a cewar Senata Hadi Sirika dake zaman dattijon da ya gabatar da sabon kudurin ke da niyyar kawo karshen bata lokaci da son zuciya yayin shari'un zaben.

“ Mutane da yawa ba su samu zuwa majalisa ba, ba su zama gwamnoni ba saboda wannan batu, kuma mun ga wannan a shari'ar janar Buhari da Obasanjo da Buhari da Yar'adua da kuma Buhari da Jonathan duk ta faru .To wannan in aka ce an sauya wannan doka cewa da farko da an je gaban alkali an ce salamu alaikum zaben da aka yi ba a yi shi bisa ka'ida ba. Sai a ce to ke hukumar zabe tun da ke kika yi wannan zabe, mallaman zabe naki ne akwatunan zabe naki ne, kuri'un ma ke ki ka bugo, form form din zaben ma naki ne ke kuma kika kulle su a inda babu wanda ya sani, to kizo ki tabbatarwa da kowa cewar wannan zabe na bisa ka'idoji da dokokin da aka shimfida.”

Kokarin bin doka ko kuma kokari na yar kiri kiri, dai zargin magudin zabe dai a baya ya kai ga tashe-tashen hankula da zub da jini ga tarrayar Najeriyar da 'yayanta kan dauki siyasa na batun ko mutuwa ko yin rai.

Abun kuma da ya sa wasu ke kallon sabon yunkurin a matsayin matakin dake iya kwantar da hankula musamman ma a bangare na adawa dake zargin jami'an na zabe da zama wani bangare na jam'iyya mai mulki a matakai na jihohi dama tarraya.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Yawancin 'yan majalisar dattawan na adawa da wannan dokaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

"Barawo ba zai kira kan shi barawo ba"

To sai dai kuma a tunanin Senator Gyang Pwajok dake zaman daya a cikin dattatwan daga Plateau, zargi na tabbatar da barawon kuri'a na a wuyan mai zargin maimakon hukumar zabe.

“ Yau in ka kama barawo ka kai shi kotu kai ne zaka nuna cewar shi ne barawo, amma ba za a zaunar da shi a ce kai barawo ka nuna mana me ya sa kai ba barawo ba, ba zai yi ba. Wanda ya ce wannan shi barawo ne shi ne ya kamata ya nunawa kotu cewar fa wannan fa shi ne barawo kuma ga abubuwan da ya yi da ya kamata a ce masa barawo”

Barawo da kaya ba shaidu, ko kuma kokari na kariya ga abokan cin mushe dai, sabuwar muhawarar dake zuwa dai dai lokacin da tarrayar Najeriya ke fara shirin wani zagayen na zabuka dai a fadar Barrister Sani Husaini Garun Gabas dake zaman wani tsohon lauyan da ya shatrafka shari'u na zabuka a gaban kotunan kasar zai zamo kafa ta kawo karshen shari'ar zabe a kasar maimakon tilasa hukumar zaben kasar ta INEC yin dai dai.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Hoto: picture-alliance/AP Photo

“Duk da cewar abun da INEC din take yi ba dai dai bane, akwai hanyoyi da yawa na kama INEC da laifi amma ba'a son yi. Wannan zai dada gurbata al'amura ne. Ina tabbatar maka cewar in aka yi wannan doka shi ke nan ma an daina tabbatar da cewar zabe bai yiwu ba ko kuma zabe ba a yishi dai dai ba domin INEC har abada ba zat a kawo maka shaidar da za ta nuna cewar ba a yi zabe dai dai ba."

Abun jira a gani dai na zaman mafita a cikin tsarin dake da burin tabbatar da gaskiya da adalci kan kowa amma kuma ya koma kafa ta son rai da biyan bukata ta 'yan kadan sakamakon tsohon tsarin shari'ar da kasar ta Najeriya ke tafe kai.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinado Abdu Waba