1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin sulhunta rikicin Japan da China

Carl Richard HolmSeptember 17, 2012

Amirka na neman shiga tsakanin a rikicin kan iyaka tsakanin Japan da China. Sakataren tsaro Leon Panetta ya yi tattakin zuwa Tokyo inda ya tattauna da takwaran aikinsa na Japan.

https://p.dw.com/p/16AAZ
U.S. Secretary of Defense Leon Panetta (R) and Japan's Minister of Defense Satoshi Morimoto smile at the end of a joint news conference at the Ministry of Defense in Tokyo, September 17, 2012. Panetta is on the first official stop of a three-nation tour to Japan, China and New Zealand. REUTERS/Larry Downing (JAPAN - Tags: POLITICS MILITARY)
Leon Panetta Satoshi Morimoto Verteidigungsministerium Tokio JapanHoto: Reuters

Sakataren tsaron Amirka Leon Panettta ya isa birnin Tokyo domin ganawa da hukumomin Japan tare da gano bakin zaren warware rikicin kan iyaka da ke tsakanin kasar da kuma China. Panetta ya ce wannan rikicin na iya haddasa yaki idan sassa biyu ba su hanzarta fahimtar juna tare da kawar da bakar gabar da ke tsakaninsu ba.

Dubban sinawa ne dai suka gudanar da zanga-zanga a sassa daban daban na kasarsu domin yin Allah wadai da yunkurin japan na abin da suka kira neman kwace wani yankin kasarsu da ke da arzikin man fetur. 'yan chinan da suka yi zanga zanga a birnin Guangzou sun kona tutar Japan tare da kutsawa cikin wani hotel da ke kusa da karamin ofishin jakadancin kasar da suke gabata da ita. yayin da a birnin Shenzen 'yan sandan kwantar da tarzoma suka yi amfani da borkona mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zanga.

Firaministan japan Yoshihiko Amano ya yi kira ga hukumomin Beijing da su kare rayukan 'yan kasarsa da kuma masana'antun 'yan kasarsa da ke da zama a China.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala