1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa a Kenya

December 27, 2007
https://p.dw.com/p/CgfX

A yau ne jamaar ƙasar Kenya suke jefa kuri’arsu a zaɓen shugaban ƙasa. Dubban masu jefa kuri’a suka yi jerin gwano a runfunan zaɓe na birane da kauyukan ƙasar domin jefa kurui’arsu a zaɓen na shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci yanzu Mwai Kibaki da Raila Odinga. An kuma girke jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a lokacin zaɓen. A jajibirin zaɓen hukumomin ƙasar sunce magoya bayan jam’iyar adawa sun jefi wasu manyan jamian ‘yan sanda uku har lahira a yammacin ƙasar suna masu zargin yan sanda da goyon bayan gwamnati wajen shirya maguɗin zaɓe.