WHO: Taron gaggawa kan cutar Coronovirus
January 30, 2020Talla
Ya zuwa yanzu cutar Coronavirus ta halaka mutane akalla 170, sama da mutane 7,000 sun harbu da cutar tun bayan tabbatar da bullar ta a tsakiyar birnin Wuhan na China a karshen shekarar 2019.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce taron wajibi ne ganin yadda aka tabbatar da cutar a kasashen Jamus da Vietnan da Japan da wasu kasashen duniya da ke cikin ko ta kwana.