1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a fara kai kayan agaji a ƙasar Siriya

December 10, 2013

Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce za su fara kai kayan agaji Siriya ta Iraƙi ta hanyar amfani da jiragen sama, nan ba da jimawa ba.

https://p.dw.com/p/1AWyl
Flüchtlinge Grenze Syrien Jordanien
Hoto: DW/K. Leigh

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira a yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka Amin Awad ne ya bayyana hakan a wannan talatar inda ya ƙara da cewar za a yi amfani da aƙalla jiragen sama bakwai daga Irbil a ƙasar don kai kayan agajin a arewa maso gabashin lardin Hesakeh na ƙasar ta Siriya.Mr. Awad ya ce sun yanke shawarar amfani da jiragen sama wajen kai kayan agajin na tsabar kuɗi dalar Amirka milyan huɗu saboda kai wa ta titunan da ke tsakanin Iraƙi da Siriya ya gaggara don 'yan tawayen Siriya na riƙe da mafi akasarin titunan.

Wannan dai shi ne karon farko da za a yi amfani da Iraƙi wajen kai wa Siriya agaji bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya da Iraƙi suka amince da yin hakan kamar dai yadda guda daga cikin mazaunnin Majalisar Nickolay Mladenov ya bayyana.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahmane Hassane