Ana dab da kaddamar da gwamnatin hadaka a sudan ta Kudu
May 2, 2019Talla
Shugaba Salva Kiir na kasar tare da jagoran 'yan tawaye Riek Machar da kuma wasu kungiyoyi ne suka haifar da jinkirta kammaluwar sulhun tun a watan Satumbar bara, duk kuwa da cewar sun gaza warware matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu da suka jefa kasar a tsaka maiwuya. Bangaren gwamnati dai ya jaddada bukatar taron ya mayar da hankali kan kafa gwamnatin hadaka, yayinda bangaren 'yan tawaye ya bukaci karin watanni shidda kafin hadakar domin samun sukunin kammala warware al'amuran tsaron da suka shafi dawowar Riek Machar kasar. Taron kammala yarjejeniyar sulhun dai zai gudana ne a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a wannan rana ta Alhamis.