1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar: Komawa kan tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza

March 2, 2024

Wata majiya daga bangaren tsaro a Masar ta tabbatar da cewa, za a dawo da tattaunanar tsagaita bude wuta a Zirin Gaza a birnin Alkahira.

https://p.dw.com/p/4d6Xz
Za a koma kan tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza
Za a koma kan tattaunawar tsagaita bude wuta a GazaHoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERS

Dama dai, Shugaba Joe Biden na Amurka ya yi fatan ganin cewa a cimma yarjejeniyar tsakanin Isra'ila da kuma kungiyar Hamas kafin ranar 10 ga watan Maris din shekarar 2024, a daidai lokacin da al'umma Musulman duniya ke fara azumin watan Ramadana. Kawo yanzu dai babu wani martani daga bangarorin biyu kan zaman sulhun da kasashen Masar da kuma Katar ke shiga tsakani.

Majiyoyin sun ce, harin da Isra'ila ta kai da ya yi sanadin rayukan Falasdinawa 100 da ke wawason neman agaji a ranar Alhamis din ya data gabata, bai mayar da hannu agogo baya ba ga tattaunawar. Kasashen duniya dai na ci gaba da matse lamba kan kulla yarjejeniyar tsagaita wuta bayan da Falasdinawa fiye da 30,000 suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kaddamar.