Za a magance ta'addanci a Najeriya
May 5, 2014Goodluck Jonathan ya dai kai ga ba da jini da zuciyarsa ga ƙoƙarin na ceto 'yan matan na Chibok, to sai dai kuma ya gaza burge al'ummar yankin arewa maso gabashin ƙasar da suka kalli kallaman shugaban ƙasar na kusan hawa biyu amma kuma suka ce shugaban ya ƙara shiga ruɗani.
Yunƙurin shugaba na kafa wani kwamitin domin tinkarar lamarin
Duk da cewar dai ya kira kafa kwamitin sannan kuma ya ambaci yiwuwar tsawaita dokar tabacin da ke jihohin yankin daga dukkan alamu da sauran tafiya a tsakanin shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan da burge al'ummar na Chibok, da ƙila ma masu adawa na ƙasar bisa matakai na gwamnatin ƙasar ga ƙoƙarin ceto yaran da ke cikin makonnin na uku ba tare da sannin halin da ko guda a cikinsu ke ciki ba.
Rashin gamsuwar sauran jama'ar ƙasar a kan ikirarin shugaban Najeriyar
Kama daga shugabanni na siyasar yankin na arewa maso gabas da ke fama da bala'in na ta'addanci ya zuwa iyayen yaran na Chibok dai sun ce ba su gamsu da alaƙawarin na gwamnatin da ta ce ta ji ta gani amma kuma ta gaza gano yaran. Senator Abdulkadir Alkali Jajere dai na zaman ɗaya a cikin 'yan majalisar dattawan ƙasar daga Yobe , kuma a faɗarsa shugaban ƙasar ya gaza amsa jerin tambayoyin da aka yi masa. “ Kusan babu wani abin da ya faɗa da ya gamsar da jama'a dangane da tamboyoyin da aka yi masa. Abin da jama'a suke buƙata shi ne a ceto yaransu da gaggawa.”
Abun jira a gani dai na zaman lokaci na cikon alƙawarin na Jonathan wanda daga dukkan alamu ke ƙara fuskantar ƙalubale mafi tada hankali ga gwamnatin da ke cika shekaru uku a wannan wata da muke ciki.
Daga ƙasa za a iza sauraron wannan rahoto
Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Usman Shehu Usman