1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a soma yin taron ƙasahen Yankin Gulf

Abdourahamane HassaneApril 21, 2016

Shugaba Barack Obama na Amirka ya gana da sarkin Salman na Saudiyya a birin Riyad inda suka tattauna tsawon saoi biyu kafin taron ƙasashen Yankin Gulf

https://p.dw.com/p/1IZT8
Saudi-Arabien König Salman empängt Barack Obama
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Obama wanda ya soma ziyara aiki ta kwanaki shida a Yankin Gabas mai nisa zai tattauna da shugabannin Yankin Gulf a taron da za soma yau,a kan batun ƙara jan ɗamar yaƙi da Ƙungiyar IS da kuma rigingimu da ake fama da su a yanki waɗanda suka haɗa da yaƙin basasa na Siriya da Yemen.

Yanzu haka dai Amirka ta ce ta aike da ƙarin sojoji kusan 220 da kuma jiragen yaƙi masu saukar ungulu,domin tallafa wa dakarun Iraƙi a kokarin da suke yi na sake ƙwato birnin Mossul birnin na biyu mafi girma na Iraƙin wanda ke ckin hanu Ƙungiyar IS tun a shekara ta 2014.