Za a tattauna batun Gambiya a Ghana
January 6, 2017Talla
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya mai shiga tsakanin a rikicin siyasa na Gambiya,inda shugaba Yahya jammeh ya fadi a zaben shugaban kasa ya yi mursisi ya ki sauka.Ya ce a gobe Asabar a wajen taron rantsar da sabon shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo a birnin Accra shugabannin kasashen na Afirka za su tattauna batun na Gambiya tare da samar da hanyoyin samun mafita a rikicin.Kakakin shugaban Najeriyar Garba Shehu wanda ya sanar da wannan labari ya ce Muhammadu Buhari ya sha alwashin warware matsalar siyasar ta Gambiya.