1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a tura sojoji yankin Kurdawa a Iraki

Yusuf Bala Nayaya
September 27, 2017

A kuri'ar jin ra'ayin jama'a kashi 93 cikin dari na Kurdawa sun zabi ballewa daga Iraki, kuri'ar raba gardama da ke fiskantar sukar mahukuntan birnin Bagadaza.

https://p.dw.com/p/2kpJw
Irak Referendum Unabhängigkeit Kurden Parlamentssitzung
Hoto: picture-alliance/abaca/M. Sudani

'Yan majalisar dokokin Iraki a ranar Laraban nan sun bukaci Firaminista Haider al-Abadi ya tura dakarun soja yankunan da Kurdawa ke da iko da su na Kirkuk, su kuma kama iko da rijiyoyin mai da ke a yankin.

Mayakan sojan Pehsmerga sun karbi iko da yankin na Kirkuk da ke da al'umma masu banbanci na kabila a shekarar 2014 lokacin da sojan Iraki suka gujewa mayakan IS da suka mamayi kashi daya bisa uku na Iraki. Mayakan a wancan lokaci sun hana dakarun IS karbar iko da rijiyoyin mai na yankin.

Wannan yanki dai da Kurdawan ke ikirarin iko da shi a tarihance ya kasance gida ga Turkawan Iraki da Larabawa. Mutanen yankin na Kurdistan na Iraki su suka kada kuri'a ta neman ficewa daga Iraki a ranar Litinin.

Matsayar da 'yan majalisar na birnin Bagadaza suka cimma a wannan rana dai ita ce filayen hakar albarkatun mai na Kirkuk za su koma karkashin iko na ma'aikatar mai ta Iraki. A kuri'ar jin ra'ayin jama'a kashi 93 cikin dari na Kurdawa sun zabi ballewa daga Iraki.