Za a yi zabe a Najeriya a Fabrairu
February 6, 2015Talla
Majalisar ƙasa ta Najeriya ta zartar da ƙudurin ci gaba da zaɓen ƙasar ba tare da an dage shi ba kamar yadda wasu ke kiraye-kirayen a yi.
Majalisar wacce ta ƙunshi manyan 'yan takara biyu a zaɓen da ke tafe da tsaffin shugabanni a Najeriya da gwamnnoni ta cimma wannan matsayar ne a ƙarshen wani taro da ta shafe yinin jiya Alhamis tana gudanarwa a fadar Aso Rock karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan.
Wasu daga cikin ƙananan jam'iyyu da mai ba da shawara ga shugaban ƙasa kan sha'anin tsaro dai a Najeriyar sun buƙaci da a dage wannan zaɓe ta yadda kowane dan ƙasar zai samu katin kaɗa ƙuri'a .
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdourahamane Hassane