za´a fara janye ma´aikatan mai dake yankin Niger Delta a Nigeria
August 23, 2006Kungiyyar kwadago ta kamfaninnikan dake hakar mai a yankin Niger Delta a Nigeria, tace zata janye ma´aikatan ta daga yankin, a sabili da rashin ingantaccen tsaro.
Kungiyoyin kwadagon biyu, sun cimma wannan yarjejeniyar ne, bayan wani taron gaggawa da suka gudanar, sakamakon wani dauki ba dadi daya gudana a tsakanin jami´an yan sanda da tsagerun yankin a farko farkon wannan mako.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa da alama wannan mataki da kungiyoyin kwadagon suka dauka ba zai rasa nasaba da yawaita garkuwa da tsagerun yankin suke da yan kasashen ketare baki dake aiki a kamfaninnikan man.
Mr Ledum Mitee, shugaban kungiyyar MOSOP, ta kwatowa yan yankin OGONI yancin su, kokawa yayi da wannan mataki da cewa ba karamar illa zai haifar ba, musanmamma a game da tattalin arzikin yankin.
A wannan shekarar dai kadai, an kiyasta cewa ma´aikatan mai sama da arba´in akayi garkuwa dasu a yankin, to sai dai an sako kusan dukkannin su, in ban da dan kasar Biritaniya da Lebanon da Amerika da Jamus da Irish da har yanzu ake ci gaba da garkuwa dasun ba.