Za'a kaɗa ƙuri'ar neman dakatar da shiri'ar shugabannin Kenya
November 13, 2013Talla
An ranar Juma'a ne in Allah ya kai mu, kwamitin sulhun MDD zai kaɗa ƙuri'ar neman kotun hukunta manyan laifuka ta MDD wato ICC, da ta dakatar da tuhumar da ake yi wa shugabannin ƙasar Kenya. Jakadan ƙasar Ruwanda a MDD Eugene Richard ya faɗawa manema labarai a birnin New York cewa, sun amince da a kaɗa kuri'a bisa daftarin da ƙungiyar Tarayyar Afirka ta bayar, na dakatar da shari'ar. Ƙuri'ar dai za a yi ta ne, da nufin tsaida shri'ar da ake yi wa shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Rotu, na aƙalla shekara guda.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu
AFP