1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za'a yi taro domin warware rikicin Siriya

May 17, 2013

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kasar Rasha sun bukaci da a gaggauta gudanar da taro domin kawo karshen rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/18aAz
Hoto: Reuters

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon da kuma Kasar Rasha sun amince da a gaggauta gudanar da taron kawo zaman lafiya a Siriya, duk kuwa da cewa Rasha tayi watsi da kiraye kirayen da kassashen Duniya keyi na ta daina taimakawa Gwamnatin Bashar Al'asad da makamai.

Ban ya tattauna da Ministan harkokin kasashen waje na Rasha Sergei Lavrov kafin daga bisani ya fara tataunawa da Shugaba Vladimir Putin na Rashan kan batun yin taro na kasa da kasa domin tattauna rikicin Siriya da zai hada bangarorin biyu dake yakar juna a karo na farko.

Sai dai Lavrov ya bayyana cewa ya zuwa yanzu yayi matukar wuri a bayyana lokacin da za'a yi taron na Geneva da ake sa ran gudanar wa a tsakiyar watan gobe, yana mai cewa ba'a shirya wadanda zasu wakilci bangarorin biyu na kasar Siriyan a taron ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman