Zabe a yanayi na fargaba a Kamaru
October 1, 2018Fiye da 'yan Kamaru miliyan shida da rabi ne za su fita kada kuri'a don zaben shugaban kasa nan gaba a wannan mako, wato a ranar Lahadi mai zuwa. Sai dai har yanzu Shugaba Paul Biya da ya jagoranci kasar tsawon shekaru 35 shi ake kallo a matsayin wanda zai yi tazarce duk da tarin kalubale da kasar ke fuskanta na masu rajin ballewa daga yankin da ke magana da harshen Turancin Ingilishi da ma masu ikirari na Jihadi.
A yankin Arewa mai Nisa, sojoji na gwabaza fada da masu ikirari na Jihadi wadanda ke da sansani a Najeriya wato Boko Haram, yayin da a bangarori biyu na masu fafutukar ballewa aka jibge jami'an na tsaro. Hakan kuwa na zuwa ne yayin da 'yan awaren masu magana da harshen Turancin Ingilishi suka yi barazanar cewa za su tada hargitsi yayin zaben na ranar bakwai ga watan nan na Oktoba da muke ciki.