Ina ra'ayin Jamusawa yan Turkiya ya karkata?
September 16, 2017Takaddamar diflomasiyya tsakanin Berlin da Ankara ta yi kamari inda har ta kai shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga Jamusawa yan asalin Turkiya kada su zabi manyan jam'iyyun siyasar kasar wadanda ya baiyana a matsayin makiyan Turkiya.
Munich na daya daga cikin biranen Jamus da ke da Jamusawa yan asalin Turkiyya da dama. Hasali ma akwai wata unguwa da ake yiwa lakabi da karamar Istanbul a kusa da babbar tashar jirgin kasa ta Munich. Ana iya samun komai na Turkawa daga shagunan Gurasa wato Kebab zuwa masu aski da masu sayar da shayi da kuma nama na Halal.
Tasirin Jamusawa yan Turkiya a zaben Jamus
Yadda Jamusawan yan asalin Turkiya za su kada kuri'a yana iya yin babban tasiri ga sakamkon zaben da za'a gudanar a ranar 24 ga watan Satumba. A tsakiyar karni na 20 ne Berlin ta gayyato Turkawa zuwa yammacin Jamus domin taimakawa sake gina kasar bayan yaki. A yau akwai jamusawa fiye da miliyan uku wadanda ke da tushe da Turkiya kuma akalla miliyan daya da dubu dari biyu sun cancanci kada kuri'a a zaben na Jamus. Sai dai kuma da yawa daga cikinsu har yanzu suna da kishin mahaifar su kuma kasarsu ta asali dama kuma goyon bayan jam'iyyar AKP ta Erdogan. Hassan Bas wani mai shagon asikin baba ne, ya zo Jamus shekaru takwas da suka wuce tare da matarsa wadda Bajamushiya ce. wannan shine karon farko da zai kada kuri'a a matsayin dan kasar Jamus.
"Yace ina da Fasfo din Jamus kuma ina da yancin kada kuri'a, amma a cikin zuciyata har yanzu ni Baturke ne. A ko da yaushe ina bin abin da ke faruwa a gida, har ma kuma a baya na zabi Erdogan da jam'iyyarsa ta AKP. Ina bin abinda su ke yi da kuma abin da shugaban kasar ya ke fada."
Hassan yace alakarsa da siyasar Turkiya a wasu lokutan ta kan haifar masa da sabani, ba ma da matarsa kadai ba, har ma da sauran yan uwansa Turkawa da ke zaune a nan Jamus. Zennap Yildizdemir daliba ce yar shekaru 25 da haihuwa ita ma ta yarda da wannan ra'ayi ta na mai cewa akan kambama bambancin ra'ayin da ke faruwa a gida a tsakanin al'ummar Turkiya da ke zaune a Jamus.
" Ta ce ka kan ji abin a jikinka. Akwai wani gungun da yake jin shi yana tare da AKP wani bangaren kuma yana kallon lamarin ta mahanga daban tare da sukar lamirin dimokradiyyar Turkiya wanda kan kai ga sabani a tsakanin iyalai da kuma abokai".
Tsamin dangantaka tsakanin Berlin da Ankara
Dangantaka dat ta yi tsami ne tsakanin Berlin da Ankara tun bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasaba ba a Turkiya a 2016. Jamus ta soki shugaba Erdogan saboda yadda yake kara zama dan mulkin kama karya musamman yadda gwamnatinsa ta kame wasu yan Jaridar Jamus da kuma yan kare hakkin dan Adam a Turkiya. Yayin da a nasa bangaren shugaba Erdogan ya zargi Jamus da nuna halayya irin ta yan Nazi bayan da kotun tsarin mulki ta haramta wa yan siyasar Turkiyya gudanar da yakin neman zabe a cikin kasar. Sai dai kuma akwai Turkawan da ke Jamus wadanda ba sa ra'ayin shugaban, kamar Meric Batica wanda aka haifa a Munich ya kuma taso a birnin.
"Yace Erdogan na iya hana wani abin da yake so. Yana kuma iya baiyana ra'ayinsa amma ba zai iya hana ni abin da nake so ba, dimokradiyya ce kuma haka ya kamata ya kasance, babu mai sauya min ra'ayi a kan wanda na ke so na zaba."
Yayin da Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel ke fatan lashe zaben na ranar 24 ga watan Satumba, a waje guda jam'iyyar ba ta da farin jini wajen Turkawa saboda adawarta ga shigar Turkiya kungiyar EU da kuma kin amincewa da izinin zama dan kasa biyu. A bisa al'ada dai Turkawan kan zabi babbar jam'iyyar adawa ta SPD. Sai dai ba'a san yadda za ta kaya ba idan Jamusawan yan asalin Turkiya suka bi umarnin Erdogan na kin zabar manyan jam'iyun ko kuma suka kauracewa zaben baki daya.