1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben jihar Thuringia ya zama mai tasiri a Jamus

Suleiman Babayo
October 26, 2019

Manyan jam'iyyun siyasa na Jamus suna gangamin karshe na yakin neman zaben jihar Thuringia da ke Jamus domin ganin jam'iyyar da za ta kafa gwamnati ta gaba a zaben da zai gudana ranar Lahadi.

https://p.dw.com/p/3RzKN
AfD Björn Höcke l Wahlkampf-Veranstaltung der AfD  in Bad Langensalz
Hoto: DW/M. Strauß

Ana gangamin karshe na yakin neman zaben jihar Thuringia da ke nan Jamus inda duk jam'iyyun siyasa ke fata bisa shawo kan masu zabe a jihar. Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel ana sa ran ta kare gangami tare da samun halartar shugabar jam'iyyar ta kasa Annegret Kramp-Karrenbauer a birnin Erfurt fadar gwamnatin jihar da yamma. Haka shugabanin sauran manyan jam'iyyun na Jamus za su halarci gangamin karshen na yakin neman zabe.

Yayin zaben na gobe Lahadi duk jam'iyyar da ta samu rinjaye a majalisar dokokin jihar ta Thuringia za ta kafa gwamnati ta gaba galibi bisa kawance da sauran jam'iyyun kamar yadda aka saba gani a kasar ta Jamus.

Ana sa ran jam'iyyar AFD mai kyamar baki za ta taka muhimmaiyar rawa yayin zaben na gobe Lahadi.