Zaben raba gardama a kasar Kenya
November 21, 2005A tun da safiyar yau litinin din ne dai Alummar kasar ta Kenya ,wadanda suka can can ci yin zabe suka fara jefa kuriun nasu game da yarda ko rashin yarda da sabon kundin tsarin mulki na kasar.
Ya zuwa yanzu dai an kiyasta cewa akwai masu sa ido daga kasashen Ketare ciki har da kungiyyar gamayyar Turai a Kalla 150, da a yanzu ke kasar ta Kenya don ganewa idon su yadda wannan zabe zai gudana.
A kuwa hasashe da ake na barkewar rikici a lokacin kada wannan kuri´a, tuni mahukuntan kasar suka dauki tsauraran matakan tsaro a gurare daban daban na kasar don tabbatar da cewa anyi wannan zabe lafiya an kuma gama lafiya.
Daukar wannan mataki dai ya biyo bayan tashe tashen hankula ne da aka fuskanta, a watan juli a lokacin da aka bayyanawa alummar kasar cewa za a samar da sabon kundin tsari mulki na kasar.
Kafin dai daukar wannan sabon mataki, kasar ta Kenya ta kasance tana amfani da kundin tsarin mulki da aka samar a tun shekara ta 1963, dai dai da lokacin da kasar ta samu yancin kai daga turawan mulkin mallaka na kasar Biritaniya.
Wannan dai sabon daftari na tsarin mulki na kunshe da dokar samar da ofishin Faraminista, wanda masu adawa suka ce dole ne a daidaita karfin mulki da za a bashi a tsakanin sa da shugaban kasa.
Kusan dai rashin jituwa da ake samu game da wannan zabe, ya ta´allaka ne akan irin karfi na mulki ko akasin haka da aka bawa ofishin shugaban kasa da Faraminista ne da aka samar a cikin sabon daftarin.
Game kuwa da wadanda suke sukar wannan mataki,jim kadan da jefa kuriar sa shugaban kasa, Mwai Kibaki ya shaidar da cewa harkokin siyasa a kasar ya shiga wani mawuyacin hali a sakamakon ire iren mutanen da suka taka rawar siyasar, amma a yanzu da alama abubuwa sun fara gyaruwa.
Za a iya gane hakan ne a cewar Kibaki, bisa la´akari da zaben raba gardama da ake yi yanzu haka a kasar a game da sabon kundin tsarin mulki da aka samar.
Ya zuwa yanzu dai rahotanni daga kasar sun shaidar da cewa da yawa daga cikin masu zabe na can cikin layi don jiran jefa kuriun nasu, to sai dai kuma akwai rahotanni dake nuna cewa a wasu tashohin an fara gudanar da magudi da kuma aringizon kuriu,wani lokacin ma a cewar bayanan har da sayen kuriun masu zabe.
Har ilya yau akwai kuma koke koke daga masu zabe cewa basu ga sunayen su a cikin rijistar zabe ba, to amma game da hakan hukumar zabe ta kasar tace an samu yan matsaloli ne nan da can amma ba anyi hakan da gangan bane.
Bugu da kari bayanai sun kara da cewa dai ,an samu gibi a cikin gwamnatin ta Kibaki dake son ganin an aiwatar da wannan sabon kundi na mulki a aikace da kuma wadanda suke adawa dashi,musanmamma a yayin da zabe na 2007 ke kara matsowa kusa.
Daga dai cikin ministocin gwamnatin ta Kibaki, akwai guda takawas da basa goyon bayan wannan sabon kundin tsarin mulkin, kuma da alama matukar Kibaki yayi nasara aka amince da wannan daftari, to babu makawa zai tsige su daga mukaman su.
Ba a da bayan haka akwai kuma hasahen cewa wannan zabe ka iya kawo baraka a tsakanin kabilun kasar, da yawan su ya tasamma miliyan 32.
Ana dai sa ran rufe tashohin zabe da misalin karfe biyar na yammacin yau litinin a kuma bayyana sakamakon zaben da zarar an kammala kidayar kuriun wala´Allah a daren yau ko kuka gobe talata, Idan Allah ya kaimu.