Zaben sabon shugaban kasar Iran
June 27, 2005Sabon shugaban kasar Iran da aka zaba, Mahmood Ahmadinejad dai na da abababn da ya fi bai wa fiffiko. Da farko, bayan tabbatad da nasarar da ya samu a zaben, Ahmadinejad ya kai ziyara ne a makabartar tsohon shugaban addinin kasar, marigayi Ayatulllah Ruhullah Khomeini, wanda shi ne ya jagoranci juyin juya halin da aka yi kasar Iran din a cikin shekarar 1979, abin da ya janyo kaddamad da jumhuriyar islama takasar. Daga bisani ne kuma, sabon shhugaban ya kai ziyarar ban girma ga shugaban addinin kasar na yanzu, Ayatullah Ali Khamenei. A jiya lahadi ne dai, Mahmood Ahmadinejad, ya bayyana a bainar jama’a a karo na farko bayan zabansa a mukamin shugaban kasar Iran da aka yi.
A ganawar da ya yi da maneman labarai dai, sabon shugaban ya yi kokarin mika sakon hannunka mai sanda ne ga kasashen ketare, musamman ma dai wadanda ke dari-dari da labarin samun nasararsa a zaben. Da yake amsa tambayar wani dan jaridar kasar Amirka, Amadinejad, ya karfafa cewa gwamnatinsa za ta kasance ta zaman lafiya ne da kuma sassaucin ra’ayi. Ya kuma yi watsi da duk wata akida ta `yan tsageru da `yan ta kife, duk da hangen da ake yi masa, musamman a kasashen yamma, na kasancewa mai bin ra’ayin `yan mazan jiya.
A kasar Iran din dai, kafar nan ta Bassiji, wato rukunin jami’an tsaro masu kula da kiyaye ka’idojin addini a bainar jama’a, ita ce aka fi sani da bin tsatsaurar ra’ayi. Wasu bangarorin kasar dai na tuhumar wannan rukunin ne da tabka magudi a zaben, don samar wa Ahmadinejad fa’idar samun nasara. Abokan hamayyarsa a zaben ma sun bayyana wannan ra’ayin.
A kan batun kare hakkin dan Adam da kuma bai wa jama’a ýancin fadar albarkacin bakinsu, shugaban mai jiran gado, ya bayyana cewa, `yanci wani tafarki ne da ke da gishiki cikin juyin juya halin islama da aka yi a kasar. Game da huldar kasarsa da Amirka kuwa, Mahmood Ahmadinenjad bai ba da wani dogon bayani ba. Tun mamaye ofishin jakadancin Amirka a birnin Teheran da aka yi, bayan juyin juya halin islama a kasar ne aka katse huldar diplomasiyya tsakanin Teheran da Washington. Takunkumin tattalin arzikin da Amirka ta sanya wa Iran din dai na janyo mata matsaloli a wannan huskar. Kazalika kuma, ana samun hauhawar tsamari tsakanin kasashen biyu, inda a wasu lokutan ma, Amirkan ke yi wa Iran din barazanar kai mata harin soji.
Sabon shugaban dai ya bayyana cewa, Iran ba ta bukatar Amirka a ko wane hali a yunkurin da take yi na ci gabanta. Sai dai ya kuma ce manufar harkokin siyasar gwamnatinsa za ta ba da fiffiko ne wajen inganta halin zaman cude-ni in cude ka da sauran kasashe, da tabbatad da adalci a huldodi tsakaninsu, da tabbatad da zaman lafiya da kuma kyautata dangantaka ta girmamawa tsakanin kasarsa da sauran kasashen duniya. A nan dai, masharhanta na ganin cewa, sabon shugaban na bin manufar siyasar da kasarsa ta shimfida ne, wadda ba ta rufe kofofinta ga kulla huldodin dangantaka da Amirka ba, amma wadda ke son ganin Amirkan ce za ta fara daukan matakin sulhu.
A kan batun shirye-shiryen makamashin nukiliyan Iran din kuwa, Ahmadinejad bai kauce daga matsayin da mahukuntan kasar suka dauka kawo yannzu ba. Ya nanata cewa, manufar mallakar makamashin nukilyan hakki ne da Iran din ke da shi, kuma za ta yi amfani da wannan fasahar ne ta hannunka mai sanda. Sabili da haka, ko kadan ba zai bari wata kasa ko wace ce ita kuma ba, ta hana Iran cin moriyar wannan hakkin. Sabili da haka, za a ci gaba da aiwatad da shirye-shiryen makamashin nukiliyan. Wannan dai na nuna cewa, Iran din za ta iya ci gaba da azurta sinadarin yureniyum, idan shawarwarin da take yi da Kungiyar Hadin Kan Turai ya ci tura. A cikin watan Satumba mai zuwa ne dai za a sake wani sabon zagaye na shawarwarin tsakanin Kungiyar Hadin Kan Turan da gwamnatin birnin Teheran.