Liberia Wahlen
November 7, 2011A wannan Talatar ne al´umar Liberiya ke zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu, to saidai ɗan takara adawa da ta kamata ya fafata da shugaba mai barin gado Ellen Sirleaf Johnson ya yanke shawara ƙauracewa wannan zaɓe, matakin da ka iya sake jefa ƙasar cikin rikicin siyasa.
Hankulan sun tashi matuƙa a Monroviya babban birnin ƙasar Liberiya.Rundunar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta baza dakarunta tare da tankokin yaƙi da kuma jiragen sama da ke shawagi, hakazalika jami´an tsaron gwamanati sun ja daga a manyan titinan birnin, domin riga kafi ga abkuwar duk wata fitina a wannan zaɓe.
An yi zagayen farko cikin kwanciyar hankali da lumana duk da cewar 'yan adawa sun yi zargin tafka maguɗi inda har ma saida ɗan takara da ya zo na biyu Winston Tubman ya yi barazana ƙauracewa zaɓen kamin daga bisani ya cenza tunani.
Amma a makon da ya gabata, ya sake ɗaukar matsayinsa na farko inda ya yi kira ga magoya bayansa su zamna gidajensu ya kuma bayyana hujjojinsa da cewa:
"Na gayyaci 'yan Liberia su tsaye gidajensu a ranar zaɓe Talata badan komai ba, face kare tsarin mulkin demokraɗiyarmu da Ellen Searlef Johnson tayi wa a karen tsaye ".
A makon da ya gabata shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta yayi murabus daga muƙaminsa domin biyan buƙatar ɗan takawar adawa dake ɗaukar sa a matsayin karen farautar gwamnati.
A nata gefe shugaba mai barin gado Ellen Sirleaf Johnson da ta samu fiye da kashi 44 cikin ɗari a zagayen farko, sannan ta samu goyan baya daga ɗan takara da ya zo na ukku, ta yi Allah wadai ga wannan mataki da abokin hamayarta ya ɗauka, wanda ta ce ya saɓawa kuɗin tsarin mulkin ƙasa:
"Ba za mu amincewa ba wani ɗan siyasa ya saka ƙasarmu cikin halin lahaula.Tubman zai ƙauracewa zaɓen badan komai ba,saboda ya riga ya sare, ya san zai shan kayi."
Ayar tambaya a yanzu itace shin ko 'yan Liberiya masu goyan bayan adawar za su karɓi kiran ƙauracewa zaɓen?
Shi dai wannan mazaunin birnin Monroviya ya ce shi kam ba zai fita zaɓe ba:
"Mu duka nan ba za mu yin zaɓe ba, domin mun yi imanin cewa akwai maguɗi a ciki saboda haka ba za mu kaɗa ƙuri´armu ba domin ɗaurewa maguɗi gindi."
Duk dai da halin ruɗamin da zaɓen ke fuskanta, hukumar zaɓe ta yanke shawara shirya shi a Talata, kenan babu tababa Ellen Sirleaf Johnson zata tazarce.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu