Harin ta'addanci a Turkiya
June 29, 2016Tuni dai gwamnatin kasar Turkiyan ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku, ga wadanda suka rasa rayukansu, sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a tashar jiragen saman Ataturk da ke birnin Santanbul ranar Talata. Ya zuwa yanzu dai, hukumomi sun sanar da cewa mutane 42 ne suka mutu sakamakon harin, yayin da wasu masu yawa suka sami raunuka. A martaninta na farko tattare da harin gwamnati a birnin Ankara ta ce wannan aiki ne na 'yan kungiyar IS masu jihadi, wadanda suka dade suna gwagwarmaya da kasar ta Turkiya. Ya zuwa yanzu dai an shaidar da gawarwakin mutane 37 daga cikinsu, wandanda suka hada har da baki 'yan kasashen ketar 10 da wasu guda biyu masu rike da paspo biyu.
Wani mutum da bom din ya tashi kan idanunsa yace akalla bama-bamai biyu ne suka tashi a tashar ta Ataturk da ke Santanbul, sa'annan daga baya aka rika jin karar bindigogi, yayin da mutane suka rika faduwa suna kwantawa a kasa cikin hali na rudani.
Hari a birni mafi girma
Tashar jiragen saman Ataturk a birnin da shi ne mafi girma a Turkiya, tana daga cikin wadanda suka fi girma da hada-hadar fasinjoji a nan nahiyar Turai, kana tana fuskantar matakan tsaro masu tsanani, musamman tun bayan hare-hare a birnin Ankara a watan Oktober na bara, inda akalla mutane 100 suka rasa rayukansu. Wani mutum da shima aka yi abin kan idanunsa, ya fadi da harshen Turkanci cewa:
"Ina isa tashar ta jiragen sama, sai na ji karar tashin bom. Na ga yadda mata da yara suke ta kara suna gudu don neman tsira, kafin jami'an tsaro su isa tashar. Na ga mutane suna ta gudu tufafin jikinsuduk sun yayyage, kuma da farko ban san cewar wannan halin ya samu ne saboda tashon bom din ba."
Shugabannin siyasa daga ko ina cikin duniya sun yi Allah wadai da tashin bom din a birnin na Santanbul. Janar sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi Allah wadai da harin, kuma ya nemi a gano wadanda suke da alhakinsa, a kuma hukunta su yadda ya dace. Kakakin fadar Amrika ta White House Josh Earnest ya ce Amerika ta yi Allah wadai da irin wannan aiki na ta'addanci.
Hari cikin watan Ramadan
Shi ma shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan a wata sanarwa ya ce harin abu ne mai muni, ganin cewar an kai shi ne a wannan wata mai tsarki na Ramadan. Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta amsa laifin kai harin na ranar Talata a babban filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin na Santanbul din. Bayan kungiyar IS da gwamnati ta ce ita ce mai laifi, gwamnatin kuma ta sha dora alhakin hare-hare a kan kungiyar nan da ke neman 'yancin cin gashin kai na yankin Kurdawa ta PKK a yankuna daban-daban na kasar ta Turkiya.