1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shiga zaman tankiya bayan gwajin makaman Koriya ta Arewa

Abdoulaye Mamane Amadou Usman Shehu
November 3, 2022

Kasashen Amirka da Japan sun yi kakkausar suka ga sabbin gwaje-gwajen makamai masu linzami ciki har da mai cin dogon zago da Koriya ta Arewa ta yi karo na biyu a cikin kwana guda.

https://p.dw.com/p/4IziE
Raketentest in Nordkorea
Hoto: Heo Ran/REUTERS

Daya daga cikin makaman ya keta har tekun Japan, lamarin da firaministan kasar Fumio Kishida ya yi Allah wadarai da shi, yana mai cewa ba za ta yiwu a zura ido kan gwaje-gwajen makamai masu linzami da Pyongyang ke ci gaba da yi ba, saboda haka dole ne duniya ta dauki mataki.

A wannan Alhamis, ma'aikatar tsaron Koriya ta Kudu ta bayyana cewa makwabciyarta Koriya ta Arewa ta yi gwajin wasu makamai guda uku, duk da yake ta ce tana da yakinin cewa gwajin bai yi wani tasiri ba.

Tuni hukumomin Seoul da na Amirka suka tabbatar da anniyarsu ta ci gaba da attisayin soji don karafafa matakan tsaro a yankin, tare da zama cikin shirin ko takwana, bayan gwaje-gwajen sabbin makaman na Koriya ta Arerwa