Harin ta'addanci ya janyo fargaba a Burkina Faso
May 13, 2019A Burkina Faso kwana daya bayan harin ta'addancin da wasu 'yan bindiga suka kai a wani cocin Katolika a yankin arewacin kasar inda suka halaka mutane shida, yanzu haka 'yan kasar sun shiga zaman zullumi a yayin da masana kan harkokin tsaro ke nuna damuwa dangane da yadda hare-haren ta'addanci ke kara yin kamari a kasar ta Burkina da ma a kasashen yankin Sahel baki daya.
A ranar Lahadin da safe a daidai lokacin da mabiya addinin Kiristan na darikar Katolika ke a tsakiyar ayyukan ibadarsu ta mako-mako, maharan su kimanin 30 dauke da bindigogi suka kutsa a cikin coci da ke a karamar hukumar Dablo ta jihar Sanmatenga a arewacin kasar inda nan take suka buda wuta kan mabiya addinin wadanda suka yi kokarin tserewa, inda suka kashe mutane shida da suka hada da limamin cocin kafin su banka wa cocin wuta. Daga nan sun kutsa a cikin gari inda suka kona shaguna da wata mashaya kana suka isa a gidan asibitin birnin, inda bayan sun yi binciken kokof suka cinna wa asibitin wuta da ma motar babban jami'in gidan likitan.
Yau shekaru hudu ke nan da Burkina Faso ke fuskantar hare-haren 'yan ta'adda, hare-haren kuma da ake dangantawa da kungiyoyin masu da'awar jihadi irin su Ansarul Islam ko kungiyar GSIM wato Groupe de Soutien a l'islam et aux Musulman da kuma kungiyar IS reshen yankin Sahara. Yanzu haka dai babbar ayar tambaya a nan ita ce wadanne kungiyoyin 'yan jihadi ne ke kaddamar da wadannan hare-hare a kasar Burkina Faso?
To sai dai Paul Melly na cibiyar binciken harkokin yau da kullum ta Chatham House da ke birnin London na kasar Birtaniya, kwararre ne kan harkokin Afirka ya ce ya zuwa yanzu ba wanda ke da amsar wannan tambaya.
"A halin da ake ciki ba iya tantance takamaimiyar kungiyar da ke kai wadannan hare-haren a kasar ta Burkina Faso ba; illa dai kawai mun san cewa a watannin baya-bayan nan kungiyoyin 'yan ta'adda da dama sun shigo kasar ta Burkina Faso."
Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin watanni biyu da kungiyoyin masu da'awar jihadi ke kai hari a kan wani coci a kasar, inda ko a ranar 29 ga watan Aprilun da ya gabata, mabiya addinin Kiristan shida suka halaka a cikin wani harin ta'addanci da aka kai a wani cocin darikar Protestan da ke a garin Silgadji na arewacin kasar.
Wani abin da ke daure wa jama'a da kai a game da ayyukan kungiyoyin masu da'awar jihadi a kasar ta Burkina Faso shi ne irin yadda suka yawaita kai hare-haren kan limaman coci da na addinin Islama da ma kuma sarakunan gargajiya da na kabilu. Mahukuntan kasar dai na zargin cewa kungiyoyin 'yan ta'addan na yin haka ne da nufin raba kawunan mabiya addinan biyu a kasar. Sai dai kuma wani babban abin tambaya shi ne irin yadda aka yi a kasashen yankin na Sahel matsalolin tsaro suka zamo tamkar ana magani kai na kaba. Paul Melly na cibiyar binciken harkokin yau da kullum ta Chatam House ya bayar da amsa yana mai cewa:
"Iyakokin kasashen Sahel kusan a bude suke, kasashen ba su da hali na iya daukar matakan tsare iyakokinsu. Abin da suke iyawa shi ne samar da 'yan sanda da sauran jami'ai da za su iya tsare bodojin shigowa kasashensu da ke a saman manyan hanyoyi. Sannan mayakan 'yan jihadi sun nakalci yankin wanda da ma ba yawan samun ruwan sama cikinsa wadanda ke ba su damar iya tafiya a saman baburra ko kuma ma a kafa ba tare da wata matsala ba."
Wannan hari dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da sojojin Faransa suka yi nasarar ceto wasu Faransawa biyu 'yan yawon buda ido daga hannun kungiyoyin 'yan jihadin da suka yi garkuwa da su bayan sato su daga kasar Benin. Wasu alkalumman kididdiga dai sun nunar da cewa daga shekara ta 2015, mutane sama da 400 suka halaka a cikin jerin hare-haren ta'addanci a kasar ta Burkina Faso.