Zambiya ta kori jakadan kasar Kuba
April 1, 2018Talla
Shi dai Vilas jakadan kasar ta Kuba a Zambiya, ya halarci bikin kaddamar da sabuwar jam'iyyar ne ta adawa a ranar Asabar a Lusaka babban birnin kasar, inda kuma ake zarginsa da furta kalamai a bainar jama'a na goyon bayan wannan sabuwar jam'iyya.
Shugaba Lungu ya nemi da kasar Kuba ta janye wannan jakada nata ta sabili da halaye da ya nuna a cewarsa da suka sha bambam da na jami'in diflomasiyya kamar yadda mai magana da yawun fadar shugaban kasar ta Zambiya ya sanar a gaban manema labarai a ranar Lahadi.