Zambiya ta yi watsi da bukatar neman mafakar siyasa
August 9, 2018Talla
Sakamakon wannan matakin watsi da bukatar mafakar siyasa da Zambiya ta yi, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana takaicin ta game da korar dan adawar Zimbabuwe Tendai Biti daga kasar ta Zambiya.
Hukumar ta ce matsantawa mai neman mafaka ya koma kasar da ya baro abu ne da ya ci karo da dokar 'yan gudun hijira ta duniya.
Ya zuwa yanzu dai shirye-shirye sun yi nisa don rantsar da Shugaba Emmerson Mnangagwa a ranar Lahadin nan mai zuwa a matsayin shugaban kasar Zimbabuwe duk kuwa da cewar shigar da karar da abokin hamayyarsa daga jam'iyyar adawa ya yi na iya haifar da tsaiko a bikin rantsuwar.