1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Saudiyya

April 10, 2011

Masu neman cenji a ƙasar Saudiyya sun bi sahun sauran ƙasashen larabawa wajen shirya zanga-zanga

https://p.dw.com/p/10r0C
Zanga-zanga a SaudiyyaHoto: AP

A ƙasar Saudiyya ɗaruruwan marasa aikin yi da ɗallibai suka shiga zanga-zanga a yau cikin birane biyu na ƙasar mai tsarki. Masu zanga-zangar su na buƙatar a samarsu aikin yi, da kuma ƙara albashin ma'aikata. Ƙasar Saudiyya wanda ita ce ta ɗaya a sayar da ɗanyan mai a duniya, ta na aiki da tsarin mulkin sarauta tsantsa, wanda ya haramta duk wata zanga zanga. A ƙasar dai babu wata jam'iyya ko majalisa, kana jaridun ƙasar duk labarin gwamnati suke bugawa. Kana rashin aikin yi ya kai kashi goma cikin ɗari a ƙasar Saudiyya, inda ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya shaida wa manema labarai cewa, zai ci gaba da zama a bakin ma'aikatar ilimin ƙasar har sai an biya masa buƙatunsa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi