Ana tuhumar 'yar jarida da laifin aikata zina
September 9, 2019Masu zanga-zangar da kungiyoyin kare hakkin bil adama, sun nemi kotun da ta gaggauta sakin 'yar jaridar Hajar Raissouni, da aka ce ta aikata zina da kuma zubar da ciki. Hajar dai ta musanta duk wadannan zarge-zargen sai dai masu shigar da kara sun ce suna da kwararan hujjoji da ke tabbatar musu ta aikata laifukan biyu da dokar kasar ta haramta.
'Yar shekaru ashirin da takwas da haihuwa tana aiki ne da wata jarida kasar mai suna Akhbar Al-Yaoum, jaridar da ta yi kaurin suna wajen yin sa-in-sa da gwamnatin kasar
Akwai yiyuwar yanke mata hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu, kamar yadda dokokin kasar ta Moroko suka tanadar wa duk wacce aka samu da laifin aikata zina ko zubar da ciki ba tare da aure ba. Wani bincike da wata kungiya mai zaman kanta ta wallafa, ya nunar cewa, a Marokon, mata tsakanin dari shida zuwa dari takwas ne ke zubar da cikin da suka dauka ba tare da suna da aure ba.