Zanga zanga saboda tsadar rayuwa a ƙasar Indiya
April 21, 2010Talla
Dubun dubatar jama'a sun gudanar da zanga zanga dangane da hauhawar frashin kayan abinci da ya ƙaru a birnin Nudeli na ƙasar Indiya. .Masu zanga zangar da suka samu goyon bayan jam'iyar adwa ta Hindu ta BJP, wace ta yi shatar mayan motoci domin yin jigilar jama'a. Sun riƙa yin kakausar suka ga gwamnastin ta Congres party a sai'ilin boren ,tare da neman ta yi marabus, saboda kasawar da suka ce ta yi wajan magance matsalar tsananin tsadar rayuwar da al umar ƙasar Indiya suka samu kansu a ciki.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala