1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman sake bude kasuwanni a Burkina Faso

Abdoulaye Mamane Amadou
April 27, 2020

Daruruan 'yan kasuwa sun gudanar da zanga-zanga a birnin Ouagadougoun Burkina Faso, da nufin tilasta wa hukumomin kasar sake bude kasuwannin da aka rufe bisa matsalar yaduwar Corona.

https://p.dw.com/p/3bUSL
Burkina Faso Ouagadougou Proteste
Hoto: Ahmed Ouoba/AFP/Getty Images

Tun a ranar 20 ga watan Aprilu ne hukumomin kasar Burkina Faso suka bayyana matakin rufe manyan kasuwannin birnin Ouagadougou da Bobo-Dioulasso birni na biyu mafi girma a kasar a wani mataki na takaita yaduwar Corona, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutun 42 a kasar.

Dauke da allunan da ke nuna fushinsu kan matakin ci gaba da rufe kasuwannin, 'yan kasuwar na Burkina Faso sun ce shirye suke da su girmamam duk wasu matakan da likitoci suka gindaya na kariya muddin hukumomin kasar suka sake bude kasuwannin.