1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar korar sojijin Faransa a Nijar

Binta Aliyu Zurmi
September 2, 2023

Rahotanni daga Nijar na cewar, daruruwan al'ummar kasar na gudanar da zanga-zangar neman fitar da sojojin Faransa daga kasar. Sama da sojiji Nijar 1,500 ne ke a Nijar.

https://p.dw.com/p/4Vshx
Niger Niamey | Demonstration von Unterstützern des Putsches vor der französischen Basis
Hoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Sojojin Faransa sun kasance a Nijar ne karkashin yarjejeniyar yaki da ta'addanci wacce sabin jagororin sojan kasar suka soke kwanaki kadan bayan karbe madafun iko. 

Kungiyoyin fararen hula a Nijar sun sha alwashin ci gaba da gudanar da wannan zanga-zangar da ma zaman dirshan har sai sojojin sun fice daga kasar.

A daya hannun kuwa Shugaba Emmanuel Macron ya zargi sojojin Nijar da yin garkuwa da Shugaba Mohamed Bazoum da har yanzu suke ci gaba da tsare shi.

Macron wanda ya bayyana cewar yana magana da Bazoum a kullum ya jaddada ci gaba da samun goyon bayan Faransa ga hambararen shugaban.