Zanga-zangar 'Yan adawa a Kenya
June 6, 2016Dubban jama'a a ne a Kenya suka gudanar da zanga-zanga a birnin Nairobi da kuma wasu sauran biranen ƙasar a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar 'yan adawa wacce ta buƙaci gwamnatin da ta rusa hukumar zaɓen ƙasar saboda zarginta da nuna fifiko ga ɓangaran gwamnatin.'Yan sandan dai sun yi amfani da kulake da kuma barkono tsohuwa wajen tarwatsa masu boren wanda aka samu asara rayuka
An kashe mutum daya kana wasu da dama suka jikkata
Wasu dubban jama'ar ke nan da ke raira kalamun sukar gwamnatin a sa'ilin zanga-zangar wacce 'yan sanda suka kashe mutum ɗaya kana aka jikkata wasu shida a garin Kisumu da ke a yammacin Kenya a lokacin da 'yan sandar suka sha arangama da masu yin gangamin waɗanda suka tarwatsa da kulake da kuma barkono.To sai dai da yake mayar da martani sepeto janar na 'yan sandar kenya Joseph Boinet ya ce sun tarwatsa zanga-zangar ne saboda haramtacciya ce.
"Kotu ta gargaɗi duk ƙungiyoyin da ke da niyar shirya-shirya zanga-zanga da su fara neman izini daga hukumomi tukuna. "
An gaza cimma sulhu tsakanin gwamnatin da 'yan adawar a kan IEBC
Tun a cikin watan Afrilun da ya gabata 'yan adawa da ƙungiyoyin farar hula ke gudanar da zanga-zanga domin tilasta wa gwamnatin ta Kenya da ta rusa hukumar zaɓen ta IEBC wacce suke zargin cewar ba za ta iya shirya sahihan zaɓuka ba da aka shirya gudanarwa a cikin watan Augusta na shekara ta 2017 a ciki har' da na shugaban ƙasa.Wanda za a sake fafatawa tsakanin shugaba Uhuru Kenyatta mai shekaru 54 da kuma jagoran 'yan adawa na ƙasar Raila Odinga ɗan shekaru 71 da haifuwa.A cikin watan Mayu da ya gabata mutane uku aka kashe a zanga-zangar da aka yi a yammacin ƙasar ta Kenya wanɗanda 'yan sanda suka harbe har lahira abin da ya janyo martani da ƙugiyoyin kare hakin bil Adama