Burkina Faso: Zargin sojoji da kashe mutane
February 3, 2023Talla
Kungiyar mai suna CISC ta fitar da wata sanarwa inda ta ce a ranar Laraba ne wasu daga cikin iyayen wadanda abin ya shafa suka sanar da ita da kashe-kashen da sojoji kasar suka yi a kauyuka uku da suka hada da Piega, Sakoani da kuma Kankangou dake kusa da Fada N'Gourma.
Kawo yanzu dai ba a sami wani martani daga bangaren sojojin ko daga gwamnatin mulkin sojan kasar kan wannan kisa ba. To sai dai kungiyar ta ce tana ci gaba da tattara bayanai kan wannan aika-aika wadanda za ta shigar nan gaba a gaban kotu.
Burkina Faso dai na fuskantar kalubalen tsaro a shekarun baya-bayanan, lamarin da ya haddasa juyin mulki sau biyu a shekarar da ta gabata.