1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zartar da hukuncin kisa akan mutum biyiu a Saudiyya

October 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bu55

A yau ne aka aiwatar da hukuncin kisa akan wasu baki yan kasashen ketare guda biyu saboda laifin yin fasa kwaurin miyagun kwayoyi a kasar Saudi Arabiya,wanda ya kawo ga adadin mutane 14 kenan,aka kashe bisa hukuncin kisa da aka yanke musu, a wannan shekara da muke ciki.Jamian kamfanin dillan labaran kasar sun sanar da mutanen da aka zartar da hukuncin akansu da kasancewa Adam bin Mohammed Ali Hassan daga tarayyar Nigeria da Mahmoud Haji Shadi daga kasar Afganistan,wanda ya gudana a birnin Jedda dake yammacin Saudiyyan.Maaikatar harkokin cikin gida na Saudiyyan dai ta sanar dacewa ,an samu mutanen biyu ne da laifuffukan yin smugan faudar Iblis ta Cocaine da ganyan Wiwi.Kasar Saudi Arabia dai na aiwatar da dokar Sharia a kasar baki daya,inda akan zartar da hukuncin kisa akan wadanada aka samu da laifin wannan hukuncin,ta hanyar fille kai da takobi.A shekarata 2005 dai mutane 86 aka aiwatar da hukuncin kisa akansu,kana a shekara ta 2004 mutane 36 .Hukuncin kisa A saudiyya kann fada kann wadanda aka samu da laifuffukan da suka hadar da kashe mutum ko yin fyade ko kuma dillancin miyagun kwayoyi da aka haramta.