1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar zazzabin denge ta yadu a Burkina Faso

Abdourahamane Hassane
November 24, 2023

Annobar zazzabin dengue, cutar da sauro ke yadawa, ta kashe mutane 356 a Burkina Faso tsakanin tsakiyar watan Oktoba zuwa tsakiyar Nuwamba.

https://p.dw.com/p/4ZQaZ
Burkina Faso Ouagadougou | Coronavirus Medizinische Versorgung
Hoto: Sam Mednick/AP Photo/picture-alliance

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce kawo yanzu tun farkon shekara mutane 570 suka mutu da zazzabin dengen a Burkina Faso. Don kokarin hana ci gaban cutar, gwamnati ta kaddamar da wani shiri na fesa maganin sauro a garuruwan biyu da abin ya fi shafa Ouagadougou da Bobo-Dioulasso.Burkina Faso na fama da zazzabin Dengue tun a shekarun ta 1960, amma a farkon shekarar ta  2017 da aka tabbatar an samu bullar cutar, inda ta kashe mutane 13.